El-Rufai ya zama Gwamnan Kaduna da ya fara yin sallah a Kafanchan tun 1974

El-Rufai ya zama Gwamnan Kaduna da ya fara yin sallah a Kafanchan tun 1974

Mun samu labari cewa Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna El-Rufai ya kafa tarihi a Jihar ta Kaduna a wannan babbar sallar bayan ziyarar da ya kai a Garin Kafanchan.

El-Rufai ya zama Gwamnan Kaduna da ya fara yin sallah a Kafanchan tun 1974
Gwamnan Kaduna yayi sallar idi a Garin Kafanchan

Gwamna Malam Nasir El-Rufai yayi sallah a Garin Kafanchan a wannan sallar inda har aka yi masa nadin sarauta. Idan ba ku manta ba an nada Gwamnan ne a matsayin Garkuwan Talakawa na Yankin Kasar Jama'a.

Kamar yadda mu ka samu labari Nasir El-Rufai ne Gwamna na farko da yayi sallar idi a Garin Kafanchan tun a lokacin wani Gwamnan Soji Janar Abba Kyari. Birgediya Abba Kyari yayi mulki ne a lokacin Shugaba Gowon.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari yace karfin sa ya dawo yanzu

A wata sallah da aka yi fiye da shekaru 44 ne Birgediya Janar Abba Kyari yayi babbar sallar idi a Garin Kafanchan. Tun bayan nan dai, a tarihi ba a kara samun Gwamnan Kaduna da yayi sallar idi a Garin na Kafanchan ba.

Idan ba ku manta ba kun ji labari Masarautar Jama’a dai ta nada Gwamna El-Rufai a matsayin Garkuwan Talakawa. Gwamnan na APC ya ziyarci Garin na Kafanchan ne domin ban-gajiya na kokarin mutanen Jihar.

Dazu ne Shugaba Buhari ya nunawa Duniya cewa har yanzu yana cikin koshin lafiya bayan da yayi doguwa tafiya bayan ya sauko da masallaci wajen sallar idi a Garin Daura.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel