Zaben maye gurbin Sanatan Bauchi: Dalilin da yasa mutanen Dogara suka ki zabar dan takarar Buhari

Zaben maye gurbin Sanatan Bauchi: Dalilin da yasa mutanen Dogara suka ki zabar dan takarar Buhari

Jama’ar karamar hukumar Bogoro a jihar Bauchi sun bayyana dalilinsu na zaben jam’iyyar PDP a zaben maye gurbin sanatan Bauchi ta kudu da aka yi sati biyu da suka wuce.

Duk da kasancewar APC ce ta samu nasara a zaben, jam’iyyar ba ta iya samun nasara a karamar hukumar Bogoro da shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara ya fito ba. Jam’iyyar PDP ta samu kuri’un da suka ninka na APC a karamar hukumar.

Shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Bogoro, Honarabul Daniel Musa, ya shaidawa jaridar Vanguard cewar Dogara bai yiwa dan takarar APC yakin neman zabe ba a mazabar sa, wata manuniya kan cewar bai damu ko ya samu nasara ko ya akasin haka ba.

Zaben maye gurbin Sanatan Bauchi: Dalilin da yasa mutanen Dogara suka ki zabar dan takarar Buhari
Yakubu Dogara

Shugaban majalisar wakilai bai fito fili ya yiwa jam’iyyar APC ko dan takarar ta yakin neman zabe ba, amma wasu sun ce ya nemi a zabi jam’iyyar APC amma bana jin hakan gaskiya ne,” a cewar Musa.

DUBA WANNAN: Sallah: Buhari ya yanka ragon layya (Hotuna)

Sannan ya cigaba da cewa, “alamu sun nuna cewa yana tare da PDP duk da hakan ba lallai ya zama gaskiya domin don da yana da alaka da jam’iyyar a Bauchi domin zai tuntube ni. Zamu so ya dawo PDP kafin zaben 2019.”

Musa ya kara da cewar jama’ar Bogoro sun zabi PDP ne saboda sabon da suka yi da jam’iyyar da kuma irin aiyukan da gwamnatocin jiha da tarayya karkashin ta suka shimfida masu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel