Mugun hali: Wata mai juna biyu ta kona mazaunan ‘yar aiki da wuka mai zafi
Ana zargin wata mata mai juna biyu, Uwargida Ogechi Maxwell, da yin amfani da wuka mai zafin gaske wajen yiwa mai yi mata aiki a gida raunuka a mazaunan ta. Lamarin ya faru ne Umuahia, babban birnin jihar Abiya.
Da take amsa laifinta, Uwargida Ogechi mai ‘ya’ya uku, ta bayyana cewar ta dora wukar ne a kan wutar risho sannan tayi amfani da ita wajen yiwa yarinya mai shekaru 11, Mary Alexander, rauni a mazaunanta saboda bata lokaci duk yayin da aka aike ta. Wani Karin laifi da saka uwargida Ogechi yiwa Mary wannan mugunta shine na rashin fahimtar yaren turanci, wanda hakan ke haifar da tangarda a sadarwa tsakaninsu.
Da take ams laifinta a shelkwatar hukumar ‘yan sanda dake Umuahia, inda kwamishinan ‘yan sandan jihar Abiya, Mista Anthony Michael Ogbizi, ya yi bajakolinta ga manema labarai, uwargida Ogechi ta bayyana cewar ta yiwa Mary din wannan hukunci ne saboda tana son take fadin gaskiya duk lokacin da ta tambaye ta.
DUBA WANNAN: Son duniya: Babban wa ya yanka kannensa biyu bayan mutuwar mahaifinsu
“Ina son take fadin gaskiyar inda take zuwa duk lokacin da na aike ta, saboda ba ta dawowa a kan lokaci. Saboda ina son ta fada min gaskiya ne shi yasa na saka wuka wuta tayi zafi sannan na dana mata a duwawunta. Duk lokacin da na aike ta tana shafe fiye da sa’a guda kafin ta dawo gida, ni kuma ina son sanin inda take zuwa.”
“Mun shafe kusan wata 8 muna tare da ita amma bayan hukuncin da nayi mata sai ta gudu. Sai bayan kwana biyu suka dawo tare da wani mutuum da ta ce min dan uwanta ne. Ni ma’aikaciyar gwamnatin jihar Abiya ce kuma ina da ‘yaya uku kuma nayi nadamar abinda na aikata,” a cewar uwargida Ogechi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng