Yaki da ta'addanci: Soji sun kashe 'yan ta'addan makiyaya 21 a jihar Benue

Yaki da ta'addanci: Soji sun kashe 'yan ta'addan makiyaya 21 a jihar Benue

- Kwamandan Operation Whirl Stroke, Janar Yekini ya ce an rasa rayyuka sakamakon arangamar da soji su kayi da makisan makiyaya a Benue da Nasarawa

- Ya ce soja guda ya riga mu gidan gaskiya yayin da wasu guda biyu sun sami raunuka sakamakon arangamar

- Kwamandan ya kuma ce akwai yiwuwar an kashe kasurgumin dan ta'adan Benue mai suna Terwase Akase wanda akafi sani da Gana a samamen da aka kai a Katsina-Alla

Hukumar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe a kalla 'yan ta'addan makiyaya 21 a jihohin Benue da Nasarawa cikin makonni kadan da suka wuce.

Punch ta wallafa cewa kwamandan Operation Whirl Stroke, Manjo Janar Adeyemi Yekini ne ya bayar da wannan sanarwan a ranar Litinin 20 ga watan Augustan shekarar 2018.

Sojin Najeriya sun kashe makiyaya 21 a jihar Benue
Sojin Najeriya sun kashe makiyaya 21 a jihar Benue

DUBA WANNAN: Bikin Sallah: Gwamna Tambuwal ya yiwa marayun Sakkwato sha tara na arziki

Ya tabbatar cewa soja guda ya rasu yayinda wasu guda biyu sun jikkata sakamakon arangamar da sojin su kayi da 'yan ta'ada a ranar Asabar da ta gabata da akayi a Gbamjimba-Akor-Tomata a karamar hukumar Guma da ke jihar Benue.

Rahoton ya ce kwamandan ya bayar da wannan bayanan ne yayin da yake yiwa manema labarai bayani a kan ayyukan rundunar ta Operation Whirl Stroke a sansanin sojin sama dake Gboko road a Makurdi babban birnin jihar Benue.

Janar Yekini ya kuma ce an kama mutane 60 da ake zargin da hannu wajen ruruta rikicin tun bayan kafa rundunar.

Kwamandan ya kuma ce akwai yiwuwar an kashe kasurgumin dan ta'adan Benue mai suna Terwase Akase wanda akafi sani da Gana a wata samame da aka kai a Tse Akwaza a karamar hukumar Katsina Alla a ranar Asabar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel