Layyar manya: Wani balarabe yayi layya da dan akuyan Riyal miliyan 13
Wani labari da muka ci karo da shi mai kama da almara da ban mamaki shine na wani balarabe dake a kasar Saudiyya da ya sayi dan akuyan Riyal miliyan 13 domin yayi layya da shi.
Idan dai aka canza kudin Riyal miliyan 13 zuwa kudin Najeriya na Naira za su kama kusan Naira biliyan daya da 'yan miliyoyi kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu ta Life In Saudi Arabia.

KU KARANTA: Wata uwa ta auri dan ta, ta bada dalili
Legit.ng ta samu cewa shi dai dan akuyan yana da wata siffa ce ta daban domin kuwa ba kasafai ake ganin irin shi ba a doron duniyar nan.
Al'ummar kasar dama duniya baki daya dai sun yi ta magana game da lamarin da har yanzu yake daukar hankali musamman ma a kafafen sadarwar zamani a ciki da wajen kasar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng