Zan lashe zabe a 2019 duk da na fice daga APC -Sanata Misau

Zan lashe zabe a 2019 duk da na fice daga APC -Sanata Misau

- Sanata Misau ya jaddada cewa har yanzu tauraruwarsa bata dusashe ba

- Ya ce zai iya lashe zaben mazabarsa ba tare da jam'iyar APC ba

- Rashin iya siyasa da nuna wariya a jam'iyar APC yasa shi ficewa daga jam'iyar

Sanata mai wakiltar mazabar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattijai, Isah Hamma Misau ya yi ikirarin cewa duk da cewar ya fice daga jam'iya mai mulki ta APC zuwa jam'iyar adawa ta PDP, tauraruwarsa bata disashe ba.

Misau yayi wannan ikirarin ne a ranar lahadi, lokacin da ya ke ganawa da dubunnan masoyanshi a sakatariyar jam'iyar PDP ta karamar hukumar Misau, inda ya karbi katin shaidar zamansa mamban jam'iyar.

A cewar sa: "Rashin iya siyasar cikin gida da kuma rashin yiwa mambobi adalci, na daga cikin da suka tursasani na fice daga jam'iyar.

KU KARANTA WANNAN: Garabasar Sallah: Masari ya baiwa kowane mahajjacin Katsina kyautar N30,000

"Ina daga cikin wadanda suka kafa jam'iyar APC, amma damu da magoya bayanmu aka mayar damu saniyar ware a zabukan jam'iyar da aka gudanar a fadin kasar. An hana mutanenmu 'form' na yin takara, tare da boye jami'an da zasu gudanar da zaben don kar mu hadu da su."

Dangane da rade radin da akeyi na cewar 'yan mazabar sanatan sun juya masa baya, Misau ya ce: "Amma yanzu zaku zama shaida ganin yadda masoyana suke kewaye da ni a yau.

"Har yanzu tauraruwata tana ci gaba da haskawa, bata dusashe ba. Zan ci zabe a mazabata ba tare da ina cikin APC ."

Domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel