Magoya bayan Buhari da Saraki sun yi arangama a filin jirgin Ilori

Magoya bayan Buhari da Saraki sun yi arangama a filin jirgin Ilori

- Siyasar 2019 ta fara tsakanin masoya yan siyasa daban-daban

- Wani bangare na yabawa Shugaban majalisar dattawa kan fito-na-fito da gwamnatin tarayya

- Irin wannan abu ya faru a filin jirgin saman jihar Kwara

Magoya baya da masoyan shugaba Muhammadu Buhari sun yi arangama da shugaban majalisar dattawa, Dakta Bukola Saraki, ranan Lahadi, 19 ga watan Agusta 2019 a babban filin jirgin saman Iliori, jihar Kwara.

Masoya Buhari sun tafi filin jirgin saman ne domin maraba da dan takaran gwamnan jihar wara karkashin jam’iyyar APC Moddibo Kawu da kuma dan takaran kujeran karkashin jam’iyyar Labour Party kawai sai sukayi arangama da yan jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP da sua zo maraba wa Bukola Saraki.

Magoya bayan Buhari da Saraki sun yi arangama a filin jirgin Ilori
Magoya bayan Buhari da Saraki sun yi arangama a filin jirgin Ilori

Ana zaune kalau sai magoya bayan Saraki suka fara wakan yabo ga shugaban majalisar. Ganin haka, sai magoya bayan Buhari suka fara iwu ‘Sai Baba’, kawai sai filin jirgin sama ya zama filin siyasa.

Da abin yayi Kamari, jami’an tsaro da manya daga cikin bangarorin biyu sukayi kokarin kwantar da kuran.

KU KARANTA: Hukumar NECO ta fitar da sakamakon jarabawar SSSCE ta 2018

Har yanzu ana takun saka tsakanin fadar shugaban kasa da majalisar dokokin tarayya kan abubuwa guda biyu.

Shugaba Buhari a karo na biyu ya yi watsi da da dokar sauya fasalin zabe da majalisar ta mika masa, hakazalika majalisa ta yi watsi da umurnin fadar shugaban kasa na su dawo majalisa don baiwa hukumar INEC damar samun kudin shirye-shiryen zaben 2019.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel