Kisan Akuyar makwabta ya jefa wata mata da 'yarta cikin matsala

Kisan Akuyar makwabta ya jefa wata mata da 'yarta cikin matsala

- Uwa da 'yayan sun gurfana gaban alkali bisa laifin hallaka Akuya

- Amma bayan karanto musu laifin da ake tuhumarsu da shi sun musanta zargin

A yau Litinin ne jami'an ‘yan sanda suka gurfanar da wata mata mai suna Eunice Nwankwo tare da yaranta uku gaban kotun yankin Mararaba dake jihar Nassarawa bisa laifin kashe Akuyar makwabciyarta.

Nwanko mai shekaru 33 a duniya tare sa kananan yaranta da suke da zama a anguwar Aso C, ana tuhumar su da tada zaune tsaye da kuma kulla munafurci.

Kisan Akuyar makwabta ya jefa wata mata da 'yarta cikin matsala
Kisan Akuyar makwabta ya jefa wata mata da 'yarta cikin matsala

Sai dai wanda ake zargin sun musanta laifin.

Mai gabatar da kara Sajan Hamen Donald, ya bayyanawa kotu cewa Rebbecca Daniel wadda suke zaune a anguwa daya da wanda ake karar ta kawo karar su ne ga ofishin ‘yan sanda dake yankin Mararaba a ranar bakwai ga watan Agustan da muke ciki.

KU KARANTA: Asirin wasu da suka dirkawa Mahaukaciya ciki a Jos ya tonu

Ya kara da cewa bayan laifin yi mata bita-da-kulli sun kashe mata Akuyarta ta wadda ta kai darajar Naira dubu 10,000.

Donald ya ce wannan laifi ya saba da kundin laifuka karkashin sashi na 96 da kuma sashi na 329.

Alkalin kotun mai shari’a Ibrahim shekarau ya bada laifin wadanda ake tuhumar bisa kudi Naira dubu 20,000 tare da kawo wanda zasu tsaya musu.

Daga cikin sharuddan belin dole ne wanda zasu tsaya musu su kasance suna zaune ne a yankin da kotun take, sannan su kasance masu abun dogaro da kansu.

Daga nan ya dage zaman kotun har sai ranar 28 ga watan Agusta.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel