Yanzu Yanzu: Buhari ya koma bakin aiki, yayi ganawar sirri da shugabannin tsaro (hotuna)
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 20 ga watan Agusta, yayi ganawar sirri tare da shuwagabannin tsaro a fadar shugaban kasa da ke Abuja, jaridar Nation ta rahoto.
A rahotanni da aka tattara, an gano cewa wannan ya kasance daya daga cikin ayyuka masu muhimmanci da shugaban kasar ya fara gudanarwa bayan dawowar shi Abuja daga hutun kwana 10 da yayi a birnin Landon.
Anyi ganawar ne a ofishin shugaban kasa da misalin karfe 11:27 na safe.
Sai dai ba a gabatar da bayanai akan dalilin da yasa aka yi ganawar sirrin mai muhimmanci ba.



KU KARANTA KUMA: Ina da kwarjinin da zan iya karawa da Buhari – Tambuwal ya maida martani ga Tinubu
A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa Buhari a yammacin Asabar, 18 ga watan Agusta, ya sauka a filin jirgin sama na Namdi Azikiwe dake Abuja bayan share kwana 10 da yayi a London.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng