Matsalar tsaro: Wata jaha a Arewacin Najeriya ta kashe bikin hawan Sallah

Matsalar tsaro: Wata jaha a Arewacin Najeriya ta kashe bikin hawan Sallah

Gwamnatin jihar Adamawa ta kashe bikin hawan Sallah da aka saba yi a jihar sakamakon matsalolin tsaro da suka yi ma jahar katutu da kuma halin da mutanen da ambaliyar ruwa ya shafa suke ciki.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito kwamishinan watsa labaru na jihar, Ahmad Sajoh ne ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 20 ga watan Agusta a babban birnin jahar, Yola.

KU KARANTA: Ikon Allah sai kallo: Wata Mata ta haifi yan 4 a sansanin yan gudun Hijira

Kwamishina Sajoh yace an yanke shawarar kashe bikin Sallar ne bayan doguwar tattaunawa da kungiyar shuwagabannin gargajiya na jihar, ya kara da cewa dukkanin bangarorin sun amince da hujjojin da aka bayyana.

“Bayan tattaunawa da shugaban kungiyar shuwagabannin gargajiya na jihar Adamawa da sauran Sarakuna, gwamnatin jihar Adamawa ta bada umarnin kashe duk wani hawan Sallah da ake yi

“An dauki wannan mataki ne saboda wasu dalilai da suka hada da matsalar tsaro da ake fama da shi a jihar da kuma halin tausayi da mutanen da ambaliyar ruwa ya shafa suke ciki, wanda yasa mutane da dama sun rasa matsuguninsu.” Inji shi.

Daga karshe kwamishina Sajoh yayi kira ga shuwagabannin gargajiya da sauran shuwagabannin al’umma dasu yi amfani da lokacin shagalin Sallah wajen wayar da kan jama’a game da muhimmancin zaman lafiya, tsaro da hadin kai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel