Ba Saraki ne ya haddasa gazawarku ba – Sanatoci ga APC

Ba Saraki ne ya haddasa gazawarku ba – Sanatoci ga APC

Shugaban kwamitin sojin ruwa na majalisar dattawa, Sanata Isah Misau, da takwaransa na kwamitin bankuna da kudi, Sanata Rafiu Ibrahim sun shawarci jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da shugabanninta da su janye daga neman wadanda zasu daurawa alhakin gazawarsu na kin cika alkawaran da suka dauka lokacin zabe ta hanyar ganin laifin shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

A wata sanarwa da Misau da Rafiu suka saki a jiya sun bayyana cewa shugabannin APC na ci gaba da yayata abunda Saraki yayi ko kuma wanda yaki yi ba tare da la’akari da cewar gwamnatin shugaba Buhari ta gaza ba.

Basa tunanin cewar hankali ba zai dauka ba danganta laifin wani ga wani wacce hakkin gwamnati ne ta cika alkawaran da ta daukarwa mutane da kanta.

Ba Saraki ne ya hadda gazawarku ba – Sanatoci ga APC
Ba Saraki ne ya hadda gazawarku ba – Sanatoci ga APC

Sunce jam’iyyar bata da cikakken wayo, sun shafe tsawon watanni 38 suna tozarta Saraki da daukar nauyin kalamun batanci akansa a kafafen yada labarai. A yanzu kuma day a sauya sheka bayan kotu ta wanke shi daga makircin da akakulla mai suna sun farad aura laifin gazaarsu akan sa.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan ta’addan Boko Haram sun yi wa wasu mutane yankan rago a Borno

Cewa tsawon shekaru uku suka yi suna kalubalantar gamnatin Goodluck Jonathan a yanzu suka ga an daina sauraron wasikar jakin da suke arantowa sai sua koma kan Saraki.

Daga karshe sun gargadi jam’iyyar akan irin abubuwan da suke zarginta da aikatawa na tozarci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel