‘Yan ta’addan Boko Haram sun yi wa wasu mutane yankan rago a Borno

‘Yan ta’addan Boko Haram sun yi wa wasu mutane yankan rago a Borno

Mun samu labari maras dadi cewa ‘Yan ta’addan Boko Haram sun yi barna a Jihar Borno inda su ka hallaka Bayin Allah ana zaune kalau yayin da al’umma ke shirin murnar bikin babbar sallah.

‘Yan ta’addan Boko Haram sun yi wa wasu mutane yankan rago a Borno
'Yan Boko Haram sun yi kaca-kaca da wani Kauye a Jihar Borno

Labari ya zo gare mu daga Jaridar Vanguard cewa ‘Yan Boko Haram sun yanka mutane 6 a wani Kauye da ke kusa da Garin Monguno. ‘Yan ta’addan sun shigo Garin ne a karshen makon can inda su ka far-ma Bayin Allah.

‘Yan ta’ddan na Boko Haram sun kama mutum 6 inda su ka yanka su kamar yadda mu ka samu labari daga Garin Maiduguri. ‘Yan ta’addan sun yi ta harbe-harbe a lokacin da su ka shiga wannan kauye mai suna Mairari.

KU KARANTA: Wata Mata ta haifi 'Yan 4 a sansanin gudun hijira

A jiya Lahadi ne aka ga gawawwakin wadannan mutane da aka yanka bayan ‘Yan ta’addan sun yi kaca-kaca da Kauyen. Kamar yadda mu ka samu labari, Jami’an tsaro dai ba su kai dauki lokacin da aka kai wannan hari ba.

Wani Bawan Allah da ya san abin da ya faru ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa ‘Yan ta’addan sun yi fiye da sa’a 2 su na wannan ta’asa inda su kashe na kashewa su ka kuma yi barna a gonakin jama’a sannan su ka sulale su ka gudu.

Dama kun ji labari cewa ana ta musayar kalamai tsakanin Gwamnatin Najeriya da Majalisar Dinkin Duniya inda ake zargin Gwamnatin kasar da bada kudi domin sakin ‘Yan Matan da aka sace kwanaki a Garin Dapchi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel