Ni Mijin Hajiya ne; Kwankwaso ya fada mana shi mijin wanene – Ganduje

Ni Mijin Hajiya ne; Kwankwaso ya fada mana shi mijin wanene – Ganduje

Mun samu wani Bidiyo daga bakin wani Hadimin Mai Girma Gwamnan Jihar Kano watau Dr. Abdullahi Umar Ganduje inda ya maidawa tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso martani na kiran sa Mijin Hajiya da yayi kwanaki.

Ni Mijin Hajiya ne; Kwankwaso ya fada mana shi mijin wanene – Ganduje
Ganduje ya kalubalanci Kwankwaso ya fadawa Duniya shi Mijin wanene

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatar da cewa shi Mijin Hajiya ne domin kuwa ya san martaba da darajar matar sa. Gwamnan ya kuma kalubalanci tsohon Gwamna Sanata Kwankwaso ya fadawa Duniya ko shi Mijin wanene.

Dr. Abdullahi Ganduje yayi wannan jawabi ne wajen wani taro na mata da aka shirya a Kano inda ya bayyana cewa ba zai soki Mai dakin Kwankwaso ba domin mutumiyar kirki ce da yake ganin mutuncin ta da kimar gidan da ta fito.

KU KARANTA:

Gwamnan na Kano ya kuma bayyana cewa shi bai damu sam don an kira sa Mijin Hajiya ba, sai dai ya nemi tsohon Mai gidan na sa da su ka samu sabani Rabiu Kwankaso ya sa wa kan sa suna da kan sa domin shi ba zai taba sa ba.

Gwamna Ganduje yayi addu’a Ubangiji ya cigaba da ba Iyalin ta Gwamna zuri’a ‘dayyiba ya na mai neman tsohon Gwamnan na Kano yayi wa jama’a bayanin wacece matar sa tun da ya soki Ganduje da cewa shi Mijin Hajiya ne.

Kwanakin baya ne Sanata Rabiu Kwankwaso ya caccaki Magajin sa Ganduje wajen kamfe din PDP da aka shirya a Mahaifar Shugaba Buhari. Kwankwaso ya fadawa mutanen Kano cewa su gaida Mijin Hajiya inda yake nufin Ganduje.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel