Gwamna Ganduje ya raba miliyan N275m ga matasa 8,800 karkashin tsarin tallafin Buhari, hotuna
A satin da ya gabata ne gwamnatin tarayya karkashin ofishin shugaba Buhari ta bayyana cewar zata raba kudi, a kokarinbnta na tallafawa masu kananun sana’o’i, domin inganta harkokin kananan sana’o’i.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewar a kalla mutane miliyan uku take saka ran zasu amfana daga wannan tsari na bayar da rancen kudi daga kowanne lungu da sako dake fadin kasar nan.
Rancen kudin ya fara ne daga N10,000 zuwa N50,000 da masu kananun sana’ar zasu amfana da shi ba tare da sun gabatar da wata kadara ko wasu takardu ba.


Daga cikin irin wannnan tsarin ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya raba N20,000 ga matasa maza zalla 8,800 masu kananun sana’o’i da suka fito daga fadin kananan hukumomin jihar 44.
DUBA WANNAN: Gudun samun matsala: PDP ta fara shirin fitar da dan takara ta hanyar sulhu daga cikin 'yan takara 12
An yi taron bayar da tallafin a gidan gwamnatin jihar Kano a jiya, Asabar.


Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng