Sojojin sama sunyi lugudan wuta a sansanin ‘yan bindiga a Zamfara

Sojojin sama sunyi lugudan wuta a sansanin ‘yan bindiga a Zamfara

- Cikin salon iya aiki Sojin saman Najeriya sun yi barin wuta a sansanonin ‘yan bindiga a jihar Zamfara

- A kwanakin baya ne dai 'yan bindigar suka addabi jihar ta Zamfara da aiyukan ta'addanci

Rundunar sojin saman kasar nan (NAF) ta bayyana tasirin da shirin atisayen 'Dirar Mikiya' yayi wajen karkade ’yan bindiga daga mabuyarsu a kauyen Shamashale da kauyen Rugu dake jihar Zamfara.

Wuta Soja: Sojojin sama sunyi lugudan wuta a sansanin ‘yan bindiga a Zamfara
Wuta Soja: Sojojin sama sunyi lugudan wuta a sansanin ‘yan bindiga a Zamfara

Hafsan Sojin saman kuma kakakin rundunar Sojin Ibikunle Daramola, shi ne ya bayyana hakan a yau Lahadi a Abuja.

Daramola ya tabbatar da cewa ‘yan bindigar suna amfani da dajin Rugu dake gabashin jihar a matsayin maboyarsu.

Kakakin Sojin ya kara da cewa harin da rundunar tasu ta kai ranar 15 ga watan Agustan da muke ciki, yana daya daga cikin shirye-shiryen da rundunar Sojin ta shirya domin dakile hare-haren da ‘yan bidigar ke kawowa, bayan wasu bayanan sirri da rundunar ta samu.

Ya ce "An tashi jiragen yaki guda biyu wadanda aka aike zuwa kai harin, da ganinsu da yawa daga cikin ‘yan bindigar suka fara guduwa da neman tsira".

"Wasu daga cikin ‘yan bindigar suna kan mashinan hawa dauke da bindigogi kirar AK47, a lokacin sai suka fara kokarin harbin jiragen".

KU KARANTA: Sojoji sun kashe wani gawurtaccen dan fashi da makami tare da kwato makamai (Hotuna)

Daramola ya kara da cewa an samu makamai da suka hada bindiga kirar AK47 guda biyu, sai bingiga kirar Machine gun, sai harsashi guda 100 mai tsayin mita 7.62 sa kuma wayar hannu guda biyu.

Mai magana da yawun rundunar yace ya kamata duk wasu yan bindigar da suka san suna dauke da makamai da su ajiye makamansu tare da mika kansu ga hukuma.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel