‘Dan Majalisa a Kasar Venezuala ya tube wandon sa ana tsakiyar zama

‘Dan Majalisa a Kasar Venezuala ya tube wandon sa ana tsakiyar zama

Mun samu labari cewa wani ‘Dan Majalisa a Kasar Venezuela yayi sintir kamar yadda Mahaifiyar sa ta haife sa a lokacin da ake wani zama mai zafi a Majalisa wanda hakan ya jawo hankalin jama'a.

‘Dan Majalisa a Kasar Venezuala ya tube wandon sa ana tsakiyar zama
Kallo ya dawo kan wani 'Dan Majalisa baya ya cire wando. Hoto: Daily Trust

Wani ‘Dan Majalisa a Kasar Venezuela mai suna Gilber Caro yayi abin da ya dauki hankalin mutane lokacin da ya tube wandon sa ana cikin tsakiyar wani zama. Caro yayi wannan ne domin nuna goyon bayan sa ga Juan Requesens.

Ana zargin wani ‘Dan adawan Kasar ta Venezuela Juan Requesens da laifin yunkurin kashe Shugaban kasa Nicolas Maduro a farkon wannan watan. ‘Dan Majalisar ya nuna cewa sharri aka kitsawa Requesens domin a ga bayan sa.

KU KARANTA: Osinbajo yayi wasu sababbin mukamai 3 a Najeriya

Yayin da ake tsakiyar wannan tattaunawa ne Gilber Caro ya tube wandon sa domin nunawa Majalisa yadda yake kishin kasar sa. Tuni dai an rufe babban ‘Dan adawa kasar Juan Requesens da laifin kokarin kashe Shugaban kasa.

Shi kan shi dai wannan ‘Dan Majalisa ya shiga gidan yari na fiye da shekara daya da rabi inda aka zarge sa da kokari tada kayar-baya a kasar. A watan Yuni ne Caro ya fito daga gidan yari a sakamakon rikicin da aka yi a kasar 2016.

Mun samu labari kuma cewa Ministan harkokin mata watau Hajiya Jummai Alhassan, ta sha da kyar a wani Kauye a cikin Jihar Taraba lokacin da ta kai ziyara a Jihar ta ta a karshen makon nan inda aka yi kaca-kaca da motar ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel