Maganar ta fito: Da kyar da jibin goshi aka cire Lawal Daura daga mukaminsa

Maganar ta fito: Da kyar da jibin goshi aka cire Lawal Daura daga mukaminsa

- Maganganun yadda aka kori shugaban DSS Lawal Daura na cigaba da fitowa

- Kamar yadda wasu suka zarga, sauran kirin korar ta gamu da cikas

- Jita-jitar samun rabuwar kai tsakanin shugaba Buhari da mataimakinsa ba gaskiya ba ne

Wasu sababbin rahotanni sun bayyana yadda shugaban kasa Muhammad Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osibanjo suka tattauna nadin shugabancin hukumar farin kaya ta kasa wato Lawal Daura da nufin sauke shi daga mukaminsa makwanni biyu kafin shugaba Buhari ya tafi hutu zuwa Landan.

Maganar ta fito: Da kyar da jibin goshi a cire Lawal Daura daga mukaminsa
Maganar ta fito: Da kyar da jibin goshi a cire Lawal Daura daga mukaminsa
Asali: UGC

Amma kokarin hakan ya kusa cin karo da matsala bayan da wasu masu fada aji suka tsoma baki akan lamarin.

Tun da farko dai shugaban da mataimakinsa sun dauki wannan matakin ne ba kamar yadda ake jita-jitar cewa babu sanin shugaban kasar dangane da korar Lawal Daura daga mukaminsa ba.

Rahotannin sun bayyana yadda shugabannin suka yi ganawar sirri tare da tattaunawa akan yadda za su sallami Lawal Dauran daga mukaminsa bisa laifuffukan da ake zarginsa da aikatawa.

Idan za'a iya tunawa dai Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya fatattaki shugaban hukumar DSS Lawal Daura ne a wata wasikar sallamar da aka mika masa, sannan aka umurce shi da ya mika ragamar mulkin ga babban darekta a hukumar.

KU KARANTA: Ministan harkokin mata Alhassan ta sha da kyar a Jihar Taraba

Kuma kafin korar Lawal Dauran sai da mataimakin shugaban kasa ya umarce shi da sufeton ‘yan sanda na kasa su bayyana a Ofishinsa, jim kadan bayan sun bayyana ne mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ya fatattake shi daga aiki.

A karshe rahotan ya bayyana cewa kawunan shugabannin hade yake kuma babu wata baraka tsakaninsu, kuma dukkan lokacin da shugaban kasa zai tafi hutu yakan mika ragamar mulkin kasar nan ne ga mataimakinsa. Wannan karon ma shugaba Buharin ya dauki wannan matakin na mika masa ragamar kasar.

Sannan sanarwar ta tabbatar da cewa akwai kyakkyawar fahimta tsakanin shugabannin biyu, kuma daukan wannan mataki da aka yi ba abu ne da za’a iya tattauna shi a gaban manema labarai ba.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel