Gwamnoni jahohi 9 da za suyi bikin sallar su ta karshe a Najeriya
Yayin da ake ta shire-shiren yin babbar sallah a sati mai kamawa, wasu gwamnoni da dama a Najeriya na shirin yin sallar su ta karshe ne a saman karagar mulki musamman ma idan akayi la'akari da cewa zaben gama gari zai zo ne a farkon shekarar 2019.
Binciken mu na tabbatar mana da cewa hasashe na nuni ne da cewa bayan wannan sallar, karamar Sallah da za ta zo idan muna da rai zata kasance ne a cikin watan Juni na shekarar 2019 bayan an yi zabe har ma an rantsar da sabbin gwamnoni.

KU KARANTA: INEC tayi karin haske game da yiwuwar daga zaben 2019
Legit.ng a binciken na ta ta tattaro mana sunayen gwamnoni musulmai da kuma suke kan wa'adin su na karshe kuma gasu kamar haka:
1. AbdulAziz Yari na jihar Zamfara,
2. Abdulfatah Ahmed na jihar Kwara,
3. Abiola Ajimobi na jihar Oyo,
4. Ibikunle Amosun na jihar Ogun,
5. Ibrahim Geidam na jihar Yobe,
6. Ibrahim Hassan Dankwambo na jihar Gombe,
7. Kashim Shettima na jihar Borno,
8. Tanko Almakura na jihar Nassarawa, da kuma
9. Ogbeni Rauf Aregebesola of Osun.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng