Babbar jam'iyyar adawa PDP ta bawa wani tsohon minista babban mukami
- Shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus ya baiwa Cif Osita Chidoka, wani babban mukami a jam'iyyar
- Jam'iyyar ta bukaci Chidoka yayi amfani da ilimin shi da kwarewar shi wurin cigaban jam'iyyar

Asali: Depositphotos
Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), Uche Secondus ya baiwa tsohon ministan jiragen sama, sannan kuma tsohon shugaban hukumar kiyaye hadura na kasa, Cif Osita Chidoka, a matsayin mai bada shawara a fannin tsare - tsare.
DUBA WANNAN: An gudu ba a tsira ba: Wani Gwamna ya gudu daga APC, PDP kuma sun ce baza su ba shi tikitin takara ba
Sanarwar ta fito daga bakin Sakataren jam'iyyar a fannin watsa labarai na kasa, Kola Ologbondiyan ranar juma'ar nan a birnin Abuja.
"Chidoka, wanda ya kware a fannin tsare - tsare na ayyukan gwamnati, muna tunanin zai yi amfani da wannan kwarewar tashi, domin ciyar da jam'iyyar mu gaba," inji shi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng