Babban Sallah: Dillalan raguna sun damu da karancin masu siya

Babban Sallah: Dillalan raguna sun damu da karancin masu siya

Gabannin bikin babban Sallah, dillalan raguna a kasuwar New Artisan dake Enugu sun koka ga karancin masu siya.

Mista Musa Yero, mukaddashin shugaban kungiyar dillalan raguna, shiyar Enugu ya alakanta lamarin ga tsadar dabobi.

Yero ya fadama kamfanin dillancin laaran Najeriya cewa farashin ya karu fiye da zaton dillalan.

Yace farashin ya karu da kusan kaso 44 cikin 100 idan aka kamanta shi da na sallan bara.

Babban Sallah: Dillalan raguna sun damu da karancin masu siya
Babban Sallah: Dillalan raguna sun damu da karancin masu siya

Tashin farashin na da nasaba da Karin kudin mota da aka samu zuwa yankin arewacin kasar.

KU KARANTA KUMA: Fashin Offa: Kotu tayi barazanar tura IGP gidan yari kan zargin saba mata

Yace ragon dan madaidaici na akan farashin naira 55,000 sabanin yadda yake a bara N35,000, yayinda manyan raguna ke zuwa tsakanin N75,000 da N95, 000 sabanin N68,000 da N73,000 da yake a bara.

Yace rago mafi karancin kudin da ake samu a kasuwa shine N24,500.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel