Janar Babangida na murnar cika shekaru 77 yau, karanta wani bangare na tarihinsa

Janar Babangida na murnar cika shekaru 77 yau, karanta wani bangare na tarihinsa

-Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya cika shekaru 77 da haihuwa yau

-Ya shugabanci Najeriya na tsawon shekaru takwas

-Gabanin saukarsa, ya soke zaben demoradiyyar aka gudanar da shekarar 1993

An haifi Janar Ibrahim Badamasi Babangida a ranan 17 ga watan Agusta 1941. Ya kasance Janar na hukumar sojin Najeriya mai murabus. Ya shugabanci Najeriya tsakanin 27 ga watan Agusta 1985 zuwa 26 ga watan Agusta 1993.

Ya rike mukamin babban hafsan sojin kasa daga watan Junairun 1982 zuwa Agusta 1985 kuma ya taa rawar gani wani juyin mulkin da ya faru a shekarun Yuli 1966, Febrairu 1976, Disamba 1983, Agusta 1985, Disamba 1985 da Afrilu 1990.

Janar Babangida na murnar cika shekaru 77 yau, karanta wani bangare na tarihinsa
Janar Babangida na murnar cika shekaru 77 yau, karanta wani bangare na tarihinsa

KU KARANTA: Har yanzu bamu wanke Saraki daga maganar Offa ba - Malami

Rawar ganin da ya taka a juyin mulkin 1966

Babangida yayinda yake Laftanan a Kaduna, ya kasance hafsoshin Arewacin Najeriyan su taka rawar gani a juyin mulkin shugaban kasan soja, Janar Aguiyi Ironsi a shekarar 1966. Kuma suka maye gurbinsa da Janar Yakubu Gowon.

Juyin mulkin Buhari a 1985

Babangida wanda ya kasance babban hafsan sojin gwamnatin Manjo Janar Muhammadu Buhari ne ya yiwa Buhari juyin mulki a ranan 27 ga watan Agusta 1985 kuma ya jefashi gidan yari.

Rayuwarsa iyalinsa

Ibrahim Badamasi Babangida ya auri marigayiya Maryam (née King) Babangida. Sun haifi yara hudu: Muhammadu, Aminu, Aishatu, and Halimatu. Maryam Babangida ta rasu ranan 27 ga watan Disamba 2009 sakamakon ciwon daji.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel