Abin takaici: An tsinci gawarwakin kananan yara biyu cikin kududufi

Abin takaici: An tsinci gawarwakin kananan yara biyu cikin kududufi

An gano gawar yara biyu a cikin wata kududufi da ke unguwar Gure ta karamar hukumar Baruten a jihar Kwara kwana daya bayan iyayen yaran sun sanar da cewa yaransu sun bata.

Punch ta ruwaito cewa an gano cewa kududufin yana da nisa sosai daga gidajen iyayen yaran.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa gawar na wani yaro ne mai suna Ibrahim Bernand wanda ke rarafe da kuma wata Aisha Micheal wadda ta fara tafiya.

An tsinci gawarwakin kananan yara cikin masai a jihar Kwara
An tsinci gawarwakin kananan yara cikin masai a jihar Kwara

Wata majiya ta bayyana cewa yaran sun bace a wurare daban-daban ne. Daya daga cikin yaran ya bace daga gida ne yayin da na biyun kuma ta bace a kasuwa.

DUBA WANNAN: Matar aure ta mutu a dakin saurayinta bayan ta gama cin amanar mijinta

Wani mazaunin unguwar ta ya bukaci a sakaya sunansa ya ce mutanen unguwar suna kyautata zaton an kashe yaran ne domin ayi amfani dasu wajen aikata tsafi.

"An saba kashe mutane saboda tsafi a nan garin; haka yasa muke tunanin akwai kashe-kashen da akeyi da mutane basu sani ba," inji shi.

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Kwara, Mr Ajayi Okasanmi ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ya ce, "Ba'a samu alamar rauni a jikin gawarwakin yaran ba. Har yanzu muna cigaba da bincike domin gano musababin mutuwarsu."

An kuma gano wasu biyu daga cikin iyayen yaran 'yan Najeriya ne amma daya daga cikin iyayen yaran 'yan kasan waje ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel