2019: Zan taka ko ina don ganin Saraki yayi nasara - Baraje
Tsohon mukaddashin shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Abubakar Kawu Baraje, yace a shirye yake ya taka rawar gani domin tabbatar da kudirin shugabancin shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.
Baraje wadda ya kasance tsohon shugaban kungiyar sabuwar APC, yace a shirye yake da ya taka ko ina domin tabbatar da nasarar Saraki a zabe ai zuwa.
Ya bayyana hakan ne a wajen taron yaye dalibai na makarantar Islamiyyar sa wanda aka gudanar a ranar Alhamis, 16 ga watan Agusta a garin Ilorin, babban birnin jihar Kwara.
![2019: Zan taka ko ina don ganin Saraki yayi nasara - Baraje 2019: Zan taka ko ina don ganin Saraki yayi nasara - Baraje](https://cdn.legit.ng/images/1120/vllkyt196mg5s447s8.jpeg?v=1)
Ya kuma bayyana cewa Saraki ya dade da kaddamar da kudirinsa na takarar kujerar shugaban kasa, cewa kuma hakan ba laifi bane domin ya dade yana renon kudirin.
KU KARANTA KUMA: Kyawawan hotunan iyalan shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, matarsa da yaransa
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki yace yana nazari akan yiwuwar tsayawarsa takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng