Wata yarinya ta kuduri aniyar kare hakkin Fulani
Ba kasafai ake samun 'yayan Fulani makiyaya da sha'awar karatun boko mai zurfi ba, to amma da alama Maryam Sa'idu Baso ta fita daban
Ba kasafai ake samun 'yayan Fulani makiyaya da sha'awar karatun boko mai zurfi ba, to amma da alama Maryam Sa'idu Baso ta fita daban. Mairo, kamar yanda ake kiranta a rigarsu ta Nyama dake garin Akwuke a jihar Enugu ta kuduri aniyar kare hakkin Fulani.
DUBA WANNAN: Kuji irin maganganu masu ratsa zuciya da Nafisa Abdullahi ta dinga yi akan gawar mahaifiyarta
Ga hirar da wakilan mu suka yi da ita.
"Sunan makarantar mu Nomadic Primary School 1, Nyama. Na fara makarantar tun daga matakin farko har zuwa aji hudu, to dana ga dai makarantar babu yawan malamai, kuma koyarwar dai akwai amma dai kadan ne, sai aka mayar dani cikin garin, yanzu ina zuwa makarantar Al-huda Arabic and Islamic Secondary School.
Ina karanta fannin kimiyya, ilimin lafiya, darusan kasuwanci, turanci, lissafi, larabci da Qur'ani da Hadisi."
Maryam ta ce babban burin ta shine ta zama lauya idan ta kammala karatun ta. Inda take cewa abinda yasa take so ta zama lauyan shine, mutanen mu suna samun matsala akan bangaren shari'a, saboda basu da wanda yayi ilimi ta fannin lauya, wanda zai iya tsaya musu. Sai dai a cikin gari akwai wadanda suke aiki da su. Saboda haka nake so na zama lauya, saboda idan na zama lauya zan iya taimakawa mutanen mu ta bangaren shari'a.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng