Boko Haram na samun kudi daga NGO da kuma satar ‘Yan mata da sauran mutane - UN

Boko Haram na samun kudi daga NGO da kuma satar ‘Yan mata da sauran mutane - UN

Mun samu labari daga Jaridar Premium Times cewa Majalisar dinkin Duniya ta bayyana yadda ‘Yan ta’addan Boko Haram da su ka fitini yankin Arewa maso Gabashin Kasar nan ke samun kudi.

Boko Haram na samun kudi daga NGO da kuma satar ‘Yan mata da sauran mutane - UN
Shugaban ‘Yan ta'addan Boko Haram Abubakar Shekau a wani bidiyo

Talaucin da yayi wa jama’a katutu a Yankin tafkin Chad yana daga cikin manyan dalilan da su ka sa ‘Yan Boko Haram ke samun Mabiya wadanda ke kai manyan hare-hare a masallatai da sauran wurare a fadin Arewacin Najeriya.

‘Yan ta’addan kan yi garkuwa da mutane ko kuma su sace kayan jama’a domin samun kudin shiga. Wani lokaci na dai ‘Yan ta’addan kan samu gudumuwa daga hannun wasu boyayyun mutane domin su cigaba da danyen aikin su.

KU KARANTA: Yemi Osinbajo ya gana da Manyan Sojojin Najeriya

Kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya watau UN ta gabatar da wata takarda kwanan nan inda ya bayyana cewa Boko Haram da kuma ‘Yan ta’addan ISIL su kan sace mutane su yi garkuwa da su domin tatsar kudi daga Bayin Allah.

Kawo yanzu dai ‘Yan Boko Haram sun yi sanadiyyar mutuwar dinbin mutane a Najeriya musamman a Yankin Adamawa da Borno da Jihar Yobe. Wasu kungiyoyi masu zaman kan-su su na cikin masu assasa ta’addancin Boko Haram.

Dama dai UN ba ta jin dadin abubuwan da su ke faruwa a halin yanzu a Najeriya musamman a bangaren sha’anin tsaro da kuma matsin tattalin arziki. ’Yan ta’addan Boko Haram na amfani da kananan yara wajen samun kudi da dasa bama-bamai

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel