Ana kukan targade: PDP ta kara yin rashin 'yan majalisa 5

Ana kukan targade: PDP ta kara yin rashin 'yan majalisa 5

Biyar daga cikin 'yan majalisar dokokin jihar Ogun daga PDP sun fita daga jam'iyyar tare da komawa wasu jam'iyyu uku.

Kakakin majalisar, Mista Suraj Adekunbi, ne ya karanta wasikun barin jam'iyyar PDP da mambobin majalisar suka mika yayin zaman majalisar na yau a Abeokuta.

Adekunbi, dan jam'iyyar APC dake wakiktar mazabar Yerwa ta arewa, ya bayyana wannan shine karo na farko da majalisar ta taba samun masu canja sheka da yawa haka.

Ana kukan targade: PDP ta kara yin rashin 'yan majalisa 5
Ana kukan targade: PDP ta kara yin rashin 'yan majalisa 5

Ya kara da cewar 'yan majalisar uku ne kawai suka canja jam'iyya a wancan zangon.

DUBA WANNAN: Kayi tsufa da mulkin Najeriya - Tambuwal ya fadawa Buhari

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar biyu daga cikin 'yan majalisar - Uwargida Akintayo Folakemi (mai wakiltar Yerwa ta kudu) da Mista Ojo Viwanu (mai wakiltar Ipokia/Idiroko) sun canja sheka daga PDP zuwa APC.

Jemili Akingbade (mai wakiltar Afon) da Atanda Razaq (mai wakiltar Yerwa arewa ta 11) sun canja sheka PDP zuwa ADC.

Mista Harrison Adeyemi (daga Ogun Waterside) ya canja sheka daga APC PDP.

Wasu daga cikin 'yan majalisar da suka fita daga PDP sun bayyana cewar sun fita daga jam'iyyar ne saboda rigingimun da take fama da su a matakin jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel