Chabdi jan: ‘Yan sanda sun yiwa wani Ango kamun kazar kuku ranar aurensa

Chabdi jan: ‘Yan sanda sun yiwa wani Ango kamun kazar kuku ranar aurensa

- Kunyar duniya wani lokaci kamar ka nitse a kasa

- Jami'an tsaro sun cafke wani mutum a gaban surikansa ranar auren

- Amma bayan an kai shi kotu, an karanto masa laifin da ake tuhumarsa da shi, sai ya ce bai san maganar ba

Wani ma’aikacin banki mai suna Aliu Mustapha ya debo rowan dafa kansa, bayan da yayi rufda ciki kan kudaden jama’a har Naira N1m.

Chabdi jan: ‘Yan sanda sun yiwa wani Ango kamun kazar kuku ranar aurensa
Chabdi jan: ‘Yan sanda sun yiwa wani Ango kamun kazar kuku ranar aurensa

Mustapha dai na aiki ne da bankin Addosser Microfinance Bank Plc, kafin ‘yan sandan su nuna masa ba sani ba sabo ta hanyar damke shi ranar aurensa, sannan suka gurfanar da shi gaban alkalin kotin dake da matsugunni a Igbosere a jihar Legas yau Alhamis.

‘Yan sanda dai sun rawaito cewa, ma’aikacin bankin mai shekaru 37 mazaunin gida mai lamba ta 8, a yankin Oremeji na jihar ta Legas sun kama shi ne ranar Asabar da ta gabata wato a ranar aurensa.

‘Yan sandan sun gabatar da shi ne gaban kotin majistiren mai shari’a Y.O. Aro-Lambo bisa tuhumar laifi guda na sata.

KU KARANTA: Rashin kudin magani ya sanya wani kashe dan uwansa mara lafiya don kowa ya huta

‘Dan sanda mai gabatar da kara Samuel Mishozunnu, ya shaidawa kotin cewa, Mustapha ya aikata laifin ne a tsakanin watan Mayu zuwa watan Yunin shekarar 2017, a lokacin yana ma’aikacin bankin Addosser Microfinance Bank Plc dake lamba 32 kan titin Lewis a jihar Legas.

An dai shaidawa kotin cewa da farko Aliu ya karbi kudin wani abokin huldar bankin har Naira N840,000, sannan ya sake karbar N160,000 amma yaki sakawa cikin asusun ajiyar wanda ya karbi kudin a wurinsa, daga bisani ya tsere.

“Tun bayan tserewarsa ne ba’a sake jin duriyarsa ba sai a loakcin da zai daura aure, hakan ta sanya ‘yan sanda suka lababa ranar bikin suka cafke shi”.

A cewar jami’i mai gabatar da karar, wannan laifin ya saba da sashi na 287(7) na kundin manyan laifuka na jihar Legas na shekarar 2015.

Sai dai gogan (Mustapha Aliu) ya kekasa kasa ya ce shi bai ma san maganar ba, don haka bai aikata laifin komai ba. Kuma nan take lauyansa M.A. Rufai ya nemi a bada shi beli.

Bayan rokon belin ne mai shari’ar ya sanya masa sharadin biyan N200,000 tare da kawo mutane biyu da zasu tsaya masa kafin ya bada shi belin. Sannan ya dage zaman kotun har sai zuwa ranar 11 ga watan Satumbar 2018.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel