An nemi makiyaya dasu daina tada zaune tsaye

An nemi makiyaya dasu daina tada zaune tsaye

- Ardon Chanchaga yayi kira ga makiyaya dasu dena tana zaune tsaye akan dan karamin abu

- Ran manomi yana matukar baci idan yaga karamin yaro da garken shanu

- Manoma su kiyaye inda makiyaya suka kebe don yin kiwo

An nemi makiyaya dasu daina tada tsaye
An nemi makiyaya dasu daina tada tsaye

Ardon Chanchaga Mallam Abdullahi Babayo, yayi kira ga makiyaya dasu dena tada zaune tsaye akan karamin abu.

Babayo shine Sarkin fulanin Chanchaga da Shaku dake Minna, yayi wannan Kira ne a lokacin da yake tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na NAN an ranar Laraba.

DUBA WANNAN: Wata Musulma 'yar Afrika ta lashe zaben fidda gwani na majalisar wakilan Amurka

Yace idan har makiyaya zasu daina amfani da wasu kananan abubuwa, hakan zai taimaka wajen rage sabani da ake samu da Manoma.

" bai kamata ya zamana yaro karami ne zai jagoranci garke guda na shanu ba.

"A duk lokacin da manomi yaga yaro Karami da garken shanu ransa yana matukar baci.

" Idan sukaga magidanci ne ke jagorancin garken hankalin su yana kwanciya domin sun tabbata shukarsu zata tsira".

Sannan yayi kira ga Manoma dasu kiyaye yin noma a inda makiyaya suka kebance domin kiwo hakan zai taimaka wajen kawo zaman lafiya tsakanin su da makiyayan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng