Mai martaba Sarkin Daura ya nada Orji Uzor Kalu wata babbar sarauta a masarautar Daura

Mai martaba Sarkin Daura ya nada Orji Uzor Kalu wata babbar sarauta a masarautar Daura

Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Farouk Umar Farouk ya yi ma tsohon gwamnan jihar Abia, kuma jigo a siyasar yankin Inyamurai da Najeriya gaba daya, Orji Uzor Kalu sarautar ‘Dan Baiwan Hausa’.

Legit.ng ta ruwaito fadar mai martaba Sarki Farouk ta sanar da haka ne cikin wata wasika data aika ma Kalu a ranar Alhamis data gabata, inda wasikar tace Sarki ya yanke shawarar nada Kalu ne sakamakon goyon bayan dayake baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: Muna shan ɗan-karan tambaya daga hannun jami’an hukumar EFCC – Inji Gwamna Samuel Ortom

Mai martaba Sarkin Daura ya nada Orji Uzor Kalu wata babbar sarauta a masarautar Daura
Mai martaba Sarkin Daura da Orji Uzor Kalu

“Ina sanar da kai game da nadin sarautar ‘Dan Baiwan Hausa’ saboda muhimmin goyon bayan da kake baiwa danmu shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma Bayajidda na biyu, haka zalika ya kawo gagarumar cigaba ga matasa, gami da cigaban da ka kawo jihar Abia.” Inji wasikar.

Daga karshe mai martaba Sarkin Daura ya yi nuni ga irin ayyukan taimako, jin kai da tallafi da Orji Kalu ke yi ma gajiyayyu mabukata ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba.

Ba wannan bane karo na farko da Kalu ke kai ziyara garin Daura na jihar Katsina, musamman tun bayan shigarsa jam'iyyar APC, don ko a karamar Sallar da ta gabata sai da ya kai ma Sarki ziyarar Sallah.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel