An nada jarumi Ali Nuhu jakadan yaki da shan miyagun kwayoyi
Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa jarumin dandalin shirya fina-finan Hausa na Kannywood da kuma na Kudu, Ali Nuhu ya samu babban matsayi.
An dai nada jarumin ne a matsayin Jakadan yaki da shan miyagun kwayoyi a karkashin gidauniyar “Big Church Foundation”.

Wannan dai ba shine karo na farko da jarumin ke samun irin wannan daukaka ba sakamakon tarin masoya da yake da shi.
KU KARANTA KUMA: Tsohon sanatan PDP ya sauya sheka zuwa APC
Ali Nuhu dai ya kasance daya daga cikin manyan jaruman fim din Hausa da zamaninsu ya haska a baya kuma yake kan haskawa, tauraron jarumin na haskawa tun zamanin da ya shiga masana’antar har izuwa yau.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng