Atiku ya sha alwashin daraja ilmi, zama a PDP da kuma yin wa’adi guda a kan mulki
Tsohon Matimakin Shugaban kasar nan watau Atiku Abubakar yana cikin masu neman takarar kujerar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar adawa ta PDP a zaben na 2019. Mun kawo wasu alkawuran da Atiku yayi game da zaben mai zuwa.
Ga wadannan alkawuran nan kamar haka:
1. Babu maganar tazarce
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar yace ba zai yi wa’adi fiye da guda a mulki ba. Atiku ya fadawa wata Jarida cewa idan ta kama a zauna a rubuta wannan yarjejeniya da shi ya yarda domin gudun saba alkawari kamar yadda Buhari yayi.
KU KARAMTA:
2. Barin Jam’iyyar PDP
A lokacin da jirgin yakin neman zaben Atiku ya shiga Garin Benin a Jihar Edo a makon nan, tsohon Mataimakin Shugaban kasar yayi alkawari cewa ko da ya sha kasa a zaben fitar da gwani na Jam’iyyar PDP ba zai sauya sheka ya bar Jam’iyyar ba.
3. Daraja harkar ilmi
Kwanaki mu ka ji labari cewa Tsohon Mataimakin Shugaban kasar nan wanda ya ke sa ran karbar mulki a 2019 yayi alkawarin cewa zai warewa harkar ilmi kashi 21% cikin kasafin kudin Najeriya idan ya zama Shugaban kasa domin mutunta karatu a kasar nan.
Kafin nan ma dai Tsohon Mataimakin Shugaban kasar dai yayi alkawari aka zabe sa a PDP zai karfafawa mata da jari domin kuwa su ne tushen kowace al’umma. Ko Atiku zai yi nasara wannan karo bayan yayi takarar Shugaban kasar sau 4 a baya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng