Abin tsoro: Mutane 7 sun mutu bayan bararrakowar wata guba
- Shakar iska mai guba yayi sanadin hallaka mutane a jihar Anambra
- Sai dai sunyi korafin gaza daukar mataki daga bangaren mahukunta
Rahotanni sun bayyana cewa a kalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu sakamakon shakar warin gurbataccen sinadarin Lignite a yankin Umuzu Mbana, Otolo Nnewi dake karamar hukumar Nnewi a jihar Anambra.
Shi dai wannan sinadari na lignite yana fitar da wata irin iskar gas ne mai warin tsiya wanda a sanadin shakarta mutane da dama sai da suka kai ga kwanciya a asibiti.
Shugaban yankin da abin ya faru Tony Afam Muodielo, shi ne wanda ya bayyana hakan, inda yace sun fara gano wannan matsalar ne tun a watan Maris din shekarar nan.
KU KARANTA: Kalli hotunan hazikan jami’an da suka kashe wata fitinanniyar gobara a Legas
"A hankali wannan abu ya cigaba da zama barazana, da farko mun so muyi amfani da wuta wajen ganin mun kawo karshen abun amma abun bai yiwuwa, sai muka yanke shawarar barin ruwan sama yayi maganun abun".
"Amma a yayin da ruwan sama ya sauka, saboda shekarar nan an samu ruwa mai yawa sai ya zama tamkar kara rura wutar abun yake".
Bayan wani ruwan sama da muka samu ranar juma'ar da ta gabata, bacci ma gagarar mu yayi a wannan yanki. Kuma abin mamaki shi ne sai muka wayi gari da daya-da-daya mutane na mutuwa".
"Cikin watanni biyu mutane bakwai sun rasu, duk da cewar bamu san dalilin mutuwarsu ba amma idan ka hada biyu da biyu kasan amsar da zaka samu. Saboda mu a wannan yankin bamu taba samun irin wannan mutuwar ba".
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng