Daga Buhari har Lalong zasu kai labari a 2019 – Kakakin majalisar dokokin jihar Plateau
Kakakin majalisar dokokin jihar Plateau, Joshua Madaki, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi nasara a zaben shugabancin kasa na 2019.
Haka zalika yace babu shakka gwamnan jihar Plateau ma, Simon Lalong zai lashe zaben jihar karo na biyu.
Kakakin majalisar dokokin jihar ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar Progressives Congress (APC) mai mulki a lokacin gangaminsu kan Ibrahim Baba Hassan, mamba mai wakiltan mazabar Jos ta arewa maso arewa a majalisar dokokin jihar.
KU KARANTA KUMA: NYSC ta saki sunayen yan bautar kasa 9 da suka nutse a ruwa a Taraba
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ga laifin wani rahoton dake cewa shi yana adawa da amfani da katin zabe da kuma na’urar tantance katin zaben a zabe mai zuwa.
Buhari a wata sanarwa a jiya ta hannun babban mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Malam Garba Shehu yace zarge-zargen cewa yaki sanya hannu a dokar da aka gabatar masa saboda yana adawa da amfani da na’urar tantance katin zabe ba gaskiya bane kuma baida tushe.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng