Hanyoyi guda uku da za abi don tabbatar da yiwuwar katin zabe

Hanyoyi guda uku da za abi don tabbatar da yiwuwar katin zabe

Akwai kwanaki kasa da 184 da suka rage domin tunkarar babban zaben shekarar 2019. Shin Ka/Kin shirya kuwa domin tunkarar wannan gagarumin zaben a matsayin Ka/Ki na dan kasa

Hanyoyi guda uku da za abi don tabbatar da yiwuwar katin zabe
Hanyoyi guda uku da za abi don tabbatar da yiwuwar katin zabe

Akwai kwanaki kasa da 184 da suka rage domin tunkarar babban zaben shekarar 2019. Shin Ka/Kin shirya kuwa domin tunkarar wannan gagarumin zaben a matsayin Ka/Ki na dan kasa?

Hanya ta farko da ya kamata ka fara bi domin ka samu ka zabi wanda ya kwanta maka a rai, ita ce ka fara mallakar katin zabe, wanda zaka iya zuwa kayi rijista a kowacce cibiya ta gabatar da katin zabe mafi kusanci da kai.

DUBA WANNAN: APC: Muna nan muna neman hanya da wasu Sanatocin PDP don tsige Saraki

Idan kuma kaje kayi katin amma ba'a baka katin zaben ka ba, akwai hanyoyi da yawa da ake bi domin tabbatar da katin zaben ka.

Babban dalilin da yasa ake so ka tabbatar da katin zaben ka shine, domin ta hakane zaka tabbatar da cewa tabbas rijistar da kayi ba a samu matsala ba, sannan kuma ta hakane zaka tabbatar da inda zaka je ka kada kuri'ar ka.

Hanyoyin da zaku bi domin tabbatar da katin zaben ku sune kamar haka:

1. Ka/Ki duba sunnan Ka/Ki a lokacin da ake nuna sunayen wadanda suka yi rijista.

2. Ka ziyarci shafin yanar gizo na hukumar zabe na kasa wato www.inecnigeria.org wannan ma wata hanya ce ta tabbatar da cewa rijistar Ka/Ki ta yiwu.

3. Sannan zaku iya tura sako na wayar hannu zuwa wannan lambar, 08171646879. Sai ka rubuta sunan jihar ka/ki, sunan mahaifi, sai kuma lambobi guda biyar na karshe da aka baka lokacin da kaje yin rijista. Misali shine kamar haka: Kano Muhammad 54321.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel