Hukumar 'yan sanda ta kori wasu jami'anta 8 da aka samu da aikata wasu manyan laifuka
Kwamishinan 'yan sandan jihar Legas, Imohimi Edgal, ya ce an sallami jami'an hukumar shida saboda samunsa da aikata wasu manyan laifuka, yayin da aka rage ma wasu shida mukaminsu.
Edgal ya ce a tsakanin watan Janairu zuwa Yulin shekarar 2018, Rundunar 'yan sanda reshen jihar Legas ta ladabatar da jami'a 108 da aka samu da aikata laifuka daban-daban.
Ya yi wannan bayanin ne a wajen taron masu ruwa da tsaki da aka shirya don bayyana ayyukan da ke wakana a hukumar a hedkwatan 'yan sandan da ke Ikeja a Legas.
Shugaban 'yan sandan ya bayar da alkaluma da ke nuna ire-iren ladabtarwar da aka yiwa jami'an hukumar da aka samu da laifuka daban-daban kama ga wadanda aka tsawata musu da kuma wadanda aka dauki wasu matakai a kansu.
DUBA WANNAN: Zamu bijrewa duk wani yunkuri na tsige Saraki - Dan majalisa
"Babu wani dan sanda da za'a daga wa kafa muddin aka same shi da laifi. Idan kayi aiki na gari kuma, za'a baka wasikar yabo ta Kwamishinan 'yan sanda.
"Bana murnar hukunta ko wane jami'i amma hakan baya nufin zamu kawar da idanun mu idan ana saba dokar aiki. Lokacin da na kama aiki a matsayin Kwamishina a Legas, na lura cewa al'umma basu karrama 'yan sanda.
"Hakan yasa na bude layin wayar tarho wanda jama'a zasu rika shigar da koke-kokensu idan wani dan sanda ya yi musu ba dai-dai ba. Mun samu korafi masu dimbin yawa."
Edgal ya yi kira da jama'an Legas su cigaba da bawa hukumar hadin kai da goyon baya ta hanyar bayar da bayyanan sirri inda ya kara da cewa jami'a 28,000 da rundunar kedashi sun wadatar domin samar da tsaro a jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng