‘Yan kasuwar Sokoto sun yi asarar Miliyan 800 a cikin tsakar dare
Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa ‘Yan kasuwar kara a Jihar Sokoto sun gamu da musibar da ta ja su kayi asarar fiye da Naira Miliyan 800 bayan gobarar dare ta rutsa da shaguna sama da 200 a makon jiya.
An dai yi asarar kusan Naira Biliyan guda a gobarar da rutsa da kasuwar dabbobi da ke cikin Garin Sokoto a Ranar Lahadin da ta gabata.Sakataren dillalan ‘Yan goro na kasuwar ya bayyana cewa wutar ta fi cin yankin ‘yan goro da kuma ledoji.
Alhaji Shine Agboola wanda yayi magana da ‘Yan jarida bayan gobarar ya tabbatar da cewa masu harkar magungunan dabbobi su na cikin wanda wannan musiba ta fi rutsawa da su. An dai taki sa’a ba a rasa ko mutum guda a gobarar ba.
KU KARANTA: 2019: Jam’iyyar APC ta ga samu ta ga rashi a Jihar Sokoto
Kaya da kudi na Naira Miliyan 800 dai su ka kone a shagunan mutane a cikin tsakiyar dare lokacin da wutar ta barke. Annobar ta auku ne a Ranar Lahadi don haka ‘Yan kasuwa da dama ba su iya kai kudin su zuwa banki ba a lokacin saboda ana hutu.
Abin ya zo da sauki domin kuwa ‘yan kwana-kwana sun yi saurin zuwa wajen aka fesa ruwa domin kashe wutar kafin barnar tayi kamari. Wata wayar wuta ce ta jawo wannan gobara inda ‘Yan kasuwar su ka nemi Gwamnati ta kawo masu dauki.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng