An rasa inda Shugaban Majalisar Wakilai ya shiga yayin da manyan APC su ka yi taro a Abuja

An rasa inda Shugaban Majalisar Wakilai ya shiga yayin da manyan APC su ka yi taro a Abuja

An yi wani babban taro na Jam’iyyar APC jiya sai dai an rasa inda Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya shiga. Kwanan nan dama ana ta jin kishin-kishin din cewa Yakubu Dogara na neman barin Jam’iyyar APC.

An rasa inda Shugaban Majalisar Wakilai ya shiga yayin da manyan APC su ka yi taro a Abuja
Da alamu cewa Dogara na shirin barin APC ya koma PDP

Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole yayi wani zama da ‘Yan Majalisar Jam’iyyar APC mai mulki a Birnin Tarayya Abuja domin ganin yadda za a dawo bakin aiki daga hutun da aka tafi a Majalisar Tarayyar.

KU KARANTA: Sanatocin APC su na neman tsige Bukola Saraki a Majalisa

Har aka yi wannan zama aka gama a otel dinnan na Sheraton da ke cikin Abuja, ba a ga sawun Yakubu Dogara ba wanda yana cikin manyan ‘Yan Jam’iyyar APC a kasar kuma shi ne Shugaban Majalisar Wakilai na Tarayyar kasar.

Rashin halartar wannan muhimmin taro ya sa ake ganin cewa babu mamaki Rt. Hon. Yakubu Dogara na shirin bin Takwaran sa Bukola Saraki ne zuwa Jam’iyyar PDP. Kwanaki ne Bukola Saraki ya bar APC don haka ake neman tsige sa.

Shugabannun Majalisar dai sun ce babu ranar dawowa aiki a makon nan. Daga cikin wanda su ka halarci taron akwai Ministan Abuja. Idan ba ku manta ba dai PDP ce ta lashe zaben Sanata na Yankin Dogara a Bauchi a makon nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng