Ba fa wai na nace sai na zama shugaban kasar Najeriya bane – Atiku

Ba fa wai na nace sai na zama shugaban kasar Najeriya bane – Atiku

A yau, Talata ne, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana cewar ba fa wai ya nace sai ya zama shugaban kasar Najeriya bane.

Atiku ya bayyana cewar ba zai fita daga jam’iyyar PDP ba koda bai samu tikitin jam’iyyar na takarar shugaban kasa ba tare da bayyana cewar da ido rufe yake neman mulkin Najeriya da tuni ya zama shugaban kasa tun a shekarar 1993.

Da yake ganawa da manema labarai bayan ganawa basaraken garin Benin, Oba Ewuare II, a cigaba da tuntubar da yake yi, Atiku ya bayyana cewar ya janyewa Abiola ne a shekarar 1993 saboda kishin kasa.

Ba fa wai na nace sai na zama shugaban kasar Najeriya bane – Atiku
Atiku

Masu yi min adawa ba abinda ba zasu fada ba, amma zan iya yin takara ko sau nawa nake so. Na cancanta kuma ina da lafiyar da zan iya shugabantar Najeriya da tsamo ta daga halin da take ciki. Mene ne laifi a yin gwaji fiye das au daya?,” a cewar Atiku.

DUBA WANNAN: Za a karrama gwamnoni 5 da suka fi kwazo wajen yiwa jama'a aiki

Ba wai ina zalamar zama shugaban kasa bane. Da ina da wannan halin da nine zan zama shugaban kasar Najeriya a shekarar 1993, amma saboda kishin kasa sai na janyewa Abiola,” in ji Atiku.

A jawabinsa, Oba Ewuare, ya bayyana cewar zai kasance mai addu’a ga Najeriya ta samu shugaba mafi alheri tare da yin kira ga ‘yan siyasa das u hada kai domin kawo matsalar tsaro dake damun mafi yawan sassan Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng