Sarkin Musulmi ya bayyana babban musabbabin mutuwar aure a tsakanin Musulmai
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya bayyana bacin ransa game da yawaitar mutuwar aure a tsakanin Musulmai, inda yace lamarin ya janyo muwahara a tsakanin jama’a saboda matsalar da yake haifarwa ga iyalai, inji rahoton jaridar Daily Trust.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sultan ya bayyana haka ne a yayin taron Malamai da hukumar Zakka da wakafi ta jihar Sakkwato ta shirya, inda yace mutuwar aure na biyo bayan almubazzarancin da ake yi a yayin bukukuwa ne.
KU KARANTA: Yan kunar bakin wake sun sabbaba mutuwar mutane 10 a Madagali
“Ya dace Malamanmu su ilimantar da jama’a game da almubazzaranci a yayin bukukuwan aure, saboda hakan na haifar da rudani dake sanadin mace macen aure a tsakanin ma’aurata.” Inji shi.
Sultan yayi kira ga Malamai dasu tabbata sun ji tsoron Allah a dukkanin ayyukansu, hakan zai samar da kyawawan halaye a tsakanin al’umma, haka zalika yayi kira ga Attajirai dasu daure su dinga taimaka ma gajiyayyu, don rage radadin halin da ake ciki.
A nasa jawabin, shugaban hukumar, Lawal Maidoki ya jinjina ma Malaman, tare da jaddada godiyarsa garesu bisa gudunmuwar da suke baiwa hukumar wajen samu nasarorinta.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng