Innalillahi-wa'inna-ilaihirraji'un: Mahaifiyar jaruma Nafisa Abdullahi ta rasu
- Mutuwa karar kwana, idan ajali yayi kira ko ba ciwo sai an je
- 'Yan wasan kwaikwayon fim din Hausa tayi rashin Uwa
A yau ne Talata ne fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Nafisa Abdullahi, ta wallafa ta shafin sada zumuntarta na Instagram da twitter cewa ta yi rashin mahaifiyarta.
Jarumar ta wallafa kamar haka; “Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un. Mun rasa komai a yau amma ba zamu tuhumi Ubangijin da ya hallice dalilin daukarki ba, domin yafi kowa kaunarki a fadin duniyar nan. Har yanzu ban gaskata abinda nake rubutawa ba." inji jarumar.
KU KARANTA: Kalli hotan kyakkyawan jaririn da aka jefar a bola
Jarumar tayi kira da jama'a su sa mahaifiyarta a cikin addu'o'i domin samun tsira da rabauta a wajen Ubangiji.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng