Gwamnatin Buhari za ta karawa Ma’aikatan Najeriya albashi a Watan Satumba
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa za a ji labarin karin albashi nan da karshen watan Satumba mai zuwa. Ministan kwadago na kasa Chris Ngige ya tabbatar da wannan a Birnin Tarayya Abuja.
A jiya Litinin ne Chris Ngige ya bayyana cewa a watan nan da za a shiga Gwamnatin Tarayya za ta sanar da karin albashin da za ayi wa Ma’aikatan Najeriya. Sanata Ngige yayi wannan bayani ne a wajen wani taro da ‘Yan kwadago su ka shirya a Abuja.
Ministan kwadagon Najeriya ya bayyanawa jama’a cewa Gwamnatin Tarayya na kokarin samawa Ma’aikatan kasar yadda za su ji dadin aiki. Ngige yace Gwamnati za ta duba lafiyar Ma’aikata da ta ‘yan uwan su har ma da walwala da jin dadin su.
KU KARANTA: An bankado wasu aika-aika da Kwankwaso yayi a Kano
Chris Ngige duk yayi wannan jawabi ne a farkon makon nan wajen wani biki da Kungiyar ‘Yan kwadagon Najeriya watau NLC ta shirya domin murnar cikar Kungiyar 40 da kafuwa. Jaridar The Tribune ta kasar ce ta rahoto wannan labari.
An dai nada kwamiti tun tuni da ke duba wannan lamari na karin albashi, ana sa rai kwanan nan za a gama aikin kuma a mikawa Gwamnati rahoto domin tabbatar da matakan da aka dauka. Har yanzu dai wasu Gwamnonin kasar ba su iya biyan albashi.
Kwanaki kun samu labari cewa Gwamna Aminu Masari na Jihar Katsina ya nemi ayi la’akari da wasu muhimman abubuwa kafin a fara maganar karin albashi a Najeriya. Gwamna yace a maida hankali kan harkar kiwon lafiya da ilmi kafin a kara albashi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng