Yanzu Yanzu: Bafarawa ya ziyarci IBB a Minna
Alhaji Attahiru Bafarawa, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party(PDP) a ranar Litilin ya ziyarci tsohon shugaban kasa a mulkin sojoji, Janar Ibrahim Babangida, a Minna.
Yusuf Abubakar, daraktan labaran kungiyar yakin neman zaben Bafarawa ne ya bayyana hakan, a ranar Talata a Abuja.
Yaa bayyana cewa ziyarar da Bafarawa ya kai Minna cigaba ne da tattaunawa akan kudirinsa na takarar shugabancin kasa a 2019.
Abubakar ya bayyana cewa Babangida da Bafarawa sun gana ne a cikin sirri a gidansa naa Hilltop.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Buhari ta gazawa yan Najeriya – Jerry Gana
Ya kuma bayyana cewa ganawar Bafarawa da Babangida ya haifar da ‘yaýa masu idanu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng