Jerin manyan mutanen da su ke da karfin fada-a-ji - FORBES

Jerin manyan mutanen da su ke da karfin fada-a-ji - FORBES

Mujallar nan ta Forbes ta fitar da jerin mutanen da su ka fi kowa karfi a Duniyar nan a wannan shekarar da ake ciki ta 2018. A jerin akwai shugabannin kasashe da shugabannin addini da kuma manyan Attajiran Duniya.

Ga dai jerin nan kamar haka:

Jerin manyan mutanen da su ke da karfin fada-a-ji - FORBES

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping tare da Takwaran sa na Koriya ta Kudu

1. Xi Jinping

Shugaban kasar Sin shi ne na farko a wannan jeri. Bincike ya nuna cewa duk Duniya babu wanda ya sha gaban sa a wajen karfen iko a halin yanzu

2. Vladimir Putin

Shugaban Rasha Putin wanda ya lashe zabe kwanan nan ya zo na 2 a wannan jeri inda ya kerewa Takwaran sa Donald Trump na kasar Amurka.

KU KARANTA: An nemi Kotu ta hana a tsige Bukola Saraki da Dogara

3. Donald Trump

Shugaba Donald Trump na Amurka ya zo na 3 a wannan jeri da Forbes ta fitar kwanaki. Yanzu haka dai Trump din yana cikin tsaka-mai-wuya a Amurka.

4. Angela Merkel

Shugaba Merkel ce macen da ta fi kowa karfi a kaf Duniya, Shugabar ta Jamus ta zo ta 4 a wannan jeri. Merkel ta dade tana mulki a Kasar Jamus da ke Turai.

Jerin manyan mutanen da su ke da karfin fada-a-ji - FORBES

Shugaban Trump yana cikin masu karfin iko a ban kasa

5. Jeff Bezos

Mai kamfanin nan na Amazon watau Jeff Bezos wanda ya ba Dala Biliyan 150 baya ya shigo cikin wannan jeri. Yanzu a Duniya kaf babu mai kudin Bezos.

Sauran wadanda su ka shiga cikin sahun 10 na farko na masu iko a Duniya sun hada da Fafaroma Francis, Attajirin Duniya Bill Gates, Sarkin Saudiyya Muhammad Bin Salman da Shugaban kasar Indiya Narenda Modi, sai kuma Larry Page.

Kwanaki kun ji labari cewa a jerin Kasashen da su kowane fama da talauci a Duniya, Kasashen Afrika ne a kan gaba. Irin wadannan kasashen sun hada da Kasar Central Africa, Burundi da Kongo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel