Alamu sun nuna kamfanin man fetur na Dangote zai kara shafe shakaru kafin ya fara aiki

Alamu sun nuna kamfanin man fetur na Dangote zai kara shafe shakaru kafin ya fara aiki

Da akwai yiwuwar kamfanin matatar man fetur da shahararren mai kudin nan Aliko Dangote yake ginawa a jihar Lagos ba za'a samu damar fara amfani dashi kamar yanda aka tsara ba

Alamu sun nuna kamfanin man fetur na Dangote zai kara shafe shakaru kafin ya fara aiki

Alamu sun nuna kamfanin man fetur na Dangote zai kara shafe shakaru kafin ya fara aiki

Da akwai yiwuwar kamfanin matatar man fetur da shahararren mai kudin nan Aliko Dangote yake ginawa a jihar Lagos ba za'a samu damar fara amfani dashi kamar yanda aka tsara ba, rahotanni sun nuna cewa matatar zata baza ta fara aiki ba sai nan da shekarar 2022, kamar yanda jaridar "Reuters" ta rawaito.

DUBA WANNAN: Yan sanda za su kama shugaban INEC, Mahmood sannan su gabatar da shi a kotu a gobe

Kamfanin wanda zai dinga samar da ganga 650,000 a kowacce rana, zai zamo kamfani mafi girma a nahiyar Afirka, ana tunanin sanadiyyar kamfanin Najeriya zata fita daga cikin halin matsalar tattalin arziki da take ciki, kuma zata tashi daga sahun kasashen da ake shigo musu da mai, zata shiga jerin kasashen da suke fitar da mai.

A watan daya gabata ne shahararren mai kudin, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyanawa jaridar Reuters cewar yana sa ran za'a kammala aikin gina matatar a shekarar 2019 sannan a fara aiki a shekarar 2020. Sai dai kuma majiyar tace, da wuya aikin ya kammala a shekarar 2022, kuma koda an gama aikin a lokacin to akwai wurare da dama a matatar da baza su fara aiki a shekarar ba.

Daraktan kamfanin na Dangote Group, Devakumar Edwin, ya bayyana cewar kamfanin akwai yiwuwar ya kai shekarar 2022 koda zai fara aiki.

"A halin da ake ciki yanzu, an kusa kammala wasu ayyuka da dama a wurin, sannan an fara gabatar da wasu a shekarar data gabata."

Dangote wanda yake tunanin kamfanin zai ci kudi kusan dala biliyan 14.

"Bai taba ganin an kammala aikin kamfanin mai girman wannan a cikin shekara biyu ba. Kamfani mai girman wannan yana bukatar a lalace a bashi shekara 5 koda kuwa za'a kammala shi," inji wata majiyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel