Rikicin Zamfara: Jami’an Yansanda sun damke yan bindiga 8 dake kai hare hare

Rikicin Zamfara: Jami’an Yansanda sun damke yan bindiga 8 dake kai hare hare

Rundunar Yansandan jihar Zamfara ta sanar da kama yan bindiga guda takwas dake da hannu cikin wani hari da yan bindiga suka kai a wata kasuwa dake garin Gurbin Bore na karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Legit.ng ta ruwaito Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Shehu Mohammed ya bayyana cewa wannan lamari ya faru ne a ranar Asabar 11 ga watan Agusta, inda wasu jama’an yankin suka tsegumta ma Yansanda cewa Yan bindiga sun kai hari kasuwar garin, har sun sace Jafar Yusuf.

KU KARANTA: Mayakan rundunar Sojan kasa sun yi bore, sun kulle filin sauka da tashin jirage na Maiduguri

“Isar Yansanda keda wuya, sai muka yi ma wurin kawanya, sa’annan muka ceto mutumin da suka sace, bugu da kari mun kama mutum takwas daga cikinsu dauke da wukake da bindigu guda biyu.” Inji shi.

Daga karshe Kaakai Shehu Mohammed yace suna binciken yan bindigan da suka kama, kum da zarar sun kammala bincikensu zasu gurfanar dasu gaban kuliyan manta sabo.

Jihar Zamfara na fama da ayyukan yan bindiga da masu garku da mutane, Idan za’a tuna a kwanakin bayan ma yan bindiga sun yi awon gaba da iyalan kwamishinan wasanni na jihar Zamfara, Abdullahi Gurbin Bore a wannan gari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel