Zamu gyara kundin tsarin mulki domin bawa Buhari damar zama shugaban kasa na dun-dun-dun - Dan takarar Sanata daga arewa
- Dan takarar Sanata a jam'iyyar APC a yankin Bauchi ta kudu, Lawal Yahaya-Gumau yace zai gabatar da kudirin dokar mayar da Buhari shugaban kasa na dun-dun-dun
- Yace yana burin zuwa majalisar dattawar ne kawai saboda kare muradun shugaba Muhammadu Buhari na daura kasa kan turbar cigaba
- A cewar Gumau, Buhari zai sauka daga kujerar shugabancin kasa ne kawai ranar da Allah ya karbi rayuwarsa
Dan takarar Sanata na jam'iyyar APC a zaben maye gurbi da za'a gudanar a ranar Asabar a yankin Bauchi ta Kudu, Lawal Yahaya-Gumau yace muddin aka zabe shi, zai mayar da hankali ne wajen yiwa kundin tsarin mulki kwaskwarima don bawa shugaba Buhari ikon zama shugaba na dun-dun-dun.
Dan takarar ya yi furta wannan kalaman ne a ranar Alhamis 9 ga watan Augusta wajen kule yakin neman zabensa a Bauchi kamar yadda Punch ta ruwaito.
Legit.ng ta gano cewa Gumau, wanda a halin yanzu yana kammala shekararsa ta takwas a majalisar wakilai na tarayya inda yake wakiltan yankin Toro yace babban dalilin da yasa yake son zuwa majalisar dattawa shine don kare maradun shugaba Muhammadu Buhari.
DUBA WANNAN: Manyan aiyuka 6 da shugaba Buhari ya yi a kowanne yankin Najeriya
Kalamansa: "Ina son ku sani cewa idan kuka bani kuri'unku a zaben da za'a gudanar a ranar Asabar, ni Lawal Yahaya-Gumau zan tafi majalisar dattawa ne don kare maradun shuguba Buhari.
"Wannan shine babban dalilin da yasa nake son zuwa majalisar tarayya tunda na sauke nauyin da kuka daura min na shekaru takwas a majalisar wakilai na tarayya.
"Da izinin Allah, zamu yi gyara cikin kundin tsarin mulki yadda shugaba Buhari zai cigaba da kasancewa kan karagar mulkinsa har iya tsawon rayuwansa. Mulkinsa zata zo karshe ne kawai ranar da Allah ya karbi rayuwarsa.
"Obasanjo ya yi iya kokarinsa don ganin ya zarce kan mulki a karo na uku amma Ubangiji bai bashi nasara ba saboda rashin kyakyawar kudirinsa. Abin da ake bukata a Najeriya yanzu shine bawa shugaba Muhammadu Buhari goyon baya kuma abinda zamu yi kenan."
Idan mai karatu bai manta ba, Legit.ng ta ruwaito cewa shugaba Muhammadu Buhari ya hallarci taron yakin neman zabe a kujerar dan majalisa mai wakiltan Bauchi ta Kudu a ranar Alhamis, 2 ga watan Augustan shekarar 2018.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng