Zabukan yau a jihohi, rahotani sunce basu yi wani armashi ba

Zabukan yau a jihohi, rahotani sunce basu yi wani armashi ba

- Noma yafi mana zabe muhimmanci

- Mazauna wani sashen jihar Bauchi sunki fita zabe

- Zaben maye gurbin Dan majalisar wakilai na jihar Bauchi ya kammala

Zabukan yau a jihohi, rahotani sunce basu yi wani armashi ba
Zabukan yau a jihohi, rahotani sunce basu yi wani armashi ba

Aiyukan noma sun sha kan al'umma mazauna kudancin Bauchi, akan haka ne ma suka tafi gona suka bar zaben maye gurbin Dan majalisar Bauchi ta kudu da akayi yau asabar.

Rahoton ofishin dillancin labarai yace har karfe 9 na safe, mutanen da suka fito aka tantance su kadan ne kuma zaben bai yi armashi ba.

A kauyen Begel na karamar hukumar Dass, wani jami'in INEC, Suleiman Abduljalal ya sanar damu cewa mutane duk sun tafi gona.

A mararabar Liman Katagum, ta karamar hukumar Bauchi da wasu kauyukan, mutanen da suka fito domin zabe basu da yawa.

Wani Agent na jam'iyyar SDP, kuma Dan asalin kauyen Begel, Abduljalal Garba ya sanar damu cewa dama halan zai iya faruwa Idan akayi zabe a lokacin damina.

"Mutane dama suna zuwa gona da safe, ko da zabe ko babu zabe, amma zasu zo kada kuri'un su zuwa yamma" ya tabbatar.

DUBA WANNAN: Ambaliya ta kashe mutum 500 a Indiya

A Tafawa-Balewa kuwa, Ezekiel Samson, manomi ne da yaje gurin kada kuri'ar da yamma, yace ya tafi gona tun safe.

"Gona farko kafin zabe."

Mutane da yawa suna gona, amma zasu dawo nan ba da dadewa ba. Inji shi

Bauchi ta kudu dai ta hada da kananan hukumomin Bauchi, Tafawa-Balewa, Toro, Dass, Bogoro, Kirfi da Alkaleri

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng