An samu barkewar takaddama a Ningxia kan rushe masallaci

An samu barkewar takaddama a Ningxia kan rushe masallaci

Dimbin al'ummar musulmi dake yammacin China na takkadama da hukumomin tsaro bayan anyi barazanar rusa masallacinsu.

Jami'an tsaron sun bayyana cewa masallacin da aka kammala gininsa cikin 'yan kwanakin nan ba shi da takardun izinin gini saboda haka za'a rushe shi.

A ranar 3 ga watan Agustan wannan shekarar ne jami'an tsaron suka fitar da wata sanarwa dake cewa dole za'a rushe masallacin saboda rashin neman izinin tsarawa da gini tun farko kamar yadda BBC ta ruwaito.

An kuma watsa sanarwan a shafukan yadda labarai da sada zumunta.

An samu barkewar takaddama a Ningxia kan rushe masallaci
An samu barkewar takaddama a Ningxia kan rushe masallaci

DUBA WANNAN: Tashin hankali: An samu biliyoyi, manyan bindigu da dubban katinan zabe a gidan Lawal Daura

Sai dai wannan lamarin bai yiwa musulman garin dadi ba kuma sunce baza su amince gwamnati ta taba masallacin ba.

Al'umma da dama sun bukaci sanin dalilin da yasa tun farko hukumomin tsaron basu tsayar da ginin masallacin ba wanda aka kammala shekaru biyu da suka gabata, in dai har da gaske ba'a bayar da izinin gina shi kamar yadda wata jaridar Hong-Kong ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da matakin hukumomin tsaron a wajen masallacin a ranar Alhamis kuma za'a cigaba a ranar Juma'a.

Hotunan dake yawo a kafafen sada zumunta sun nuna dandazon mutane masu zanga-zanga a gaban masallacin.

A halin yanzu dai ba'a san ko hukumomin tsaron zasu fara rushe masallacin a ranar Juma'a kamar yadda suka tsara ko kuma zasu canja shawara sakamakon korafin da musulmin garin keyi kan lamarin.

A yayin da ake wannan takkadamar, kafar yadda labaran kasar China ba tace uffan ba kan lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng