Osinbajo mutun ne mai biyayya da rikon amana – Sarkin Daura
A wata sanarwa daga Laolu Akande, babban mai ba shugaban kasa shawara a harkokin labarai da jama’a, a ofishin mataimakin shugaban kasa yace Faruk ya fadi hakan ne a lokacin da Osinbajo ya kai masa ziyarar ban girma a fadarsa a ranar Alhamis.
An bayyana jawabin ne a Abuja a ranar Juma’a.
Sarkin ya nuna godiya ga mukaddashin shugaban kasar bisa goyon bayan da yake ba shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan masarautar.
KU KARANTA KUMA: Masu son ganin fadowar Saraki makiyan damokradiya ne – Gwamna Ortom
Yace ba’a taba samun irin wannan gwamnati da shugaban kasa da mataimakinsa ked a fahimtan juna da mutunta juna ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng