Yanzu Yanzu: Dole a tsige Saraki - Oshimhole

Yanzu Yanzu: Dole a tsige Saraki - Oshimhole

Adams Oshiomhole, shugaban jam’iyyar Progressives Congress (APC) na kasa, yace babu makawa sa an tsigeshugaban majalisar dattawa Bukola Saraki.

Da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Juma’a, 10 ga watan Agusta, Oshiomhole yace bayan tsige Saraki jam’iyyar zata yi kokari don tabbatar da cewa an kayar da shi a mazabarsa a 2019.

Yace za’a lalata daular siyasar Saraki a jiha Kwara.

Yanzu Yanzu: Dole a tsge Saraki - Oshimhole

Yanzu Yanzu: Dole a tsge Saraki - Oshimhole
Source: Depositphotos

Jam’iyya mai mulki ta sanyawa shugaban majalisar dattawa zafi akan ya sauka daga kan matsayinsa bayan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) amma Saraki ya sha alwashin cigaba da kasancewa akan kujerarsa.

KU KARANTA KUMA: Ministan lafiya ya je garin Yola don ganin Duduwale mutumin da ya je Abuja da kafa don rantsar da Buhari (hotuna)

A wani taron manema labarai da akayi a ranar Laraba Saraki yace zai sauka daga matsayinsa ne kawai idan kaso biyu cikin uku na majalisar dattawa suka cire shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel